Gwamnatin jihar Adamawa ta tabbatar da mutuwar mutane 10 a wata mummunar ambaliyar ruwa data afku sakamakon mamakon ruwan sama.
Mazauna yankin sun bayyana cewa, ambaliyar ruwan ta rutsa da wasu kauyukan dake bakin koguna a karamar hukumar Girei, inda ta yi barna a gine-gine da filayen noma.
KARANTA WANNAN LABARIN: Likitoci Masu Neman Kwarewa Sun Tsawaita Yajin Aiki
Sakataren zartarwa na Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Adamawa (ADSEMA), Dr Sulaiman Muhammad ya ce adadin mutanen da suka rasa matsugunansu ya kai 2,538.
Ya ce hukumar za ta kwashi kayayyakin agaji ta dunguma zuwa yankunan da abin ya shafa domin taimakawa wadanda suka rasa matsugunansu.
Muhammad ya ce “har yanzu ba a gano gawarwaki uku ba yayin da aka sallami wasu ‘yan mata uku da suka jikkata daga asibiti.”
Ya ce galibin mutanen Jabi Lamba da sauran kauyukan suna zaune ne a gidajen ‘yan uwansu.
A wani labarin kuma Dan Bindiga Bello Turji Ya Rungumi Shirin Zaman Lafiya A Zamfara
Wani kasurgumin dan bindiga Bello Turji ya rungumi shirin zaman lafiya na gwamnatin jihar Zamfara a wani yunkuri na kawo karshen ‘yan fashi da makami a yankin arewa maso yamma.
Mataimakin gwamnan jihar Zamfara Sanata Hassan Nasiha ne ya bayyana hakan a yayin wani taro kan harkokin tsaro da kungiyar dalibai ta jami’ar Madina ta shirya a Gusau babban birnin jihar.