Mai Martaba Shehun Borno Alhaji Abubakar Ibn Umar Garba Al-amin El-Kanemi a ranar Laraba, yace shirin da ake yi na maido da tubabbun ƴan Boko Haram cikin jama’a abun murna ne, idan har hakan zai kawo zaman lafiya a ƙasar.
Uban Ƙasar yayi jawabi ne a lokacin taron gangamin amincewa da da sasanci da maido da tubabbun ƴan ta’adda da masu taimaka masu a Maiduguri.
Yace ƴan ta’adda a Jahar sun daɗe suna aikata munanan ayyuka kuma suka tuba, a dalilin haka al’umma sun amince domin karɓar sasanci da ƙoƙarin maido da zaman lafiya, kamar yadda majiyar jaridar Dimokuraɗiyyar ta ruwaita.
KARANTA WANNAN LABARIN: Osun: ‘Yan Sanda Sun Cafke Wadanda Ake Zargi Da Kashe ‘Yan Asalin Garin Modakeke
Ya kara dacewa, tubabbun ƴan Boko Haram tuni sun gane laifuffukan su, sai yayi kiran samar da dauwammen zaman lafiya.
Yace “matsalar ƴan Boko Haram abune da kowa ya riga ya sani, kuma aka daɗe ana yaƙi dashi na tsawon lokaci, idan wannan zai sa a zo ƙarshe, to gaskiya muna masa marhaba.
“A sani na, dukkanin masu ruwa da tsaki a Borno, ciki harda hakimai da dagattai, gami da shuwagabannin addini, sun amince da cewa, sasanci abune da ake buƙata ga dukkanin kowa da kowa.”
Mai Martaba sarkin, ya buƙaci hukumomi da suyi aiki kafaɗa da kafaɗa, da ƙananan hukumomin su, da hakimai da dagattai, domin tabbatar da shirin samar da dauwammen zaman lafiya.
Kwamishinan yaɗa labaru da al’adu na Jahar Alhaji Babakura Abba Joto, yace kimanin ƴan boko haram dubu 6,000 suka miƙa wuya, amma ba za’a tura su zuwa cikin mutane ba, har sai an tantance tuban su.
Kwamishinar Harkokin Mata da walwalar jama’a Hajiya Zuwaira Gambo tace da yawa daga cikin matan da suka tuba, basu shiga cikin harkar ta’addancin ba, amma ƴan ta’addan suka tilasta masu zama a wajen su.