Akalla mutane 6,000 ne suka karbi Naira 20,000 kowannensu a matsayin tallafin kudi a Katsina a wani bangare na kokarin gwamnatin tarayya na rage radadin talauci a tsakanin talakawa da marasa galihu a kasar nan. Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito
Hakazalika, sama da iyalai 1,000 a jihar ne suka ci gajiyar abinci da kayan abinci a matsayin tallafin da gwamnatin tarayya ke yi ga wadanda ambaliyar ruwa ta shafa a jihar.
Ministar kula da jin kai da magance iftila’i da ci gaban jama’a Hajiya Sadiya Umar Farouq ce ta bayyana hakan a unguwar Mazoji da ke Daura, yayin da ta kaddamar da rabon kayayyakin tallafin.
KARANTA WANNAN LABARIN: Ambaliyar Ruwa Ta Kashe Mutum 7 A Jihar Neja
Kana ta ce wasu mutane 500 sun ci gajiyar aikin jinya kyauta, inda aka yi masu maganin matsalolin ciwon ido daban-daban tare da baiwa marasa lafiya da suka amfana kyauta da magunguna da sauran kayayyaki masu mahimmanci kamar gilashin ido da ke taimakawa mutum wajen gani.
Ministan ya ce gwamnatin tarayya tare da hadin gwiwar gwamnatocin jihohi suna gudanar da tantance bukatu da suka shafi bala’in ambaliyar ruwa da ya rutsa da yawancin jihohin tarayyar kasar nan, da nufin tallafa wa wadanda abin ya shafa.
A WANI LABARIN KUMA: Yan Bindiga Sun farmaki Wani Masallaci Tare Da Sace Masallata
Wasu ‘yan bindiga sun yi awon gaba da wasu masu ibada a wani masallacin Juma’a da ke unguwar Zugu a karamar hukumar Gummi ta jihar Zamfara.
Mazauna yankin sun ce ‘yan bindigar sun boye bindigunsu a cikin tufafin su, inda suka kutsa cikin masallacin a lokacin da Limamin zai fara gabatar da huduba.