Gwamnatin tarayya ta sanar da baiwa wasu ‘yan kasashen waje dari biyu da tamanin da shida (286) takardar shaidar zama dan kasa da suka fito daga kasashe arba’in da tara.
Daily Post ta ruwaito cewa, Babban sakatare na ma’aikatar harkokin cikin gida, Dr Shuaib Belgore, ne ya bayyana hakan a cikin wata talla da ya sanyawa hannu kuma aka bai wa manema labarai a ranar Asabar.
KARANTA WANNAN LABARIN: Yar Shekara 13 ta Rubuta Tare da Haddace Alqur’ani Hizufi 60
Sanarwar ta nuna cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da bayar da takardar shaidar zama dan Najeriyan ne a watan Fabrairun wannan shekara.
A cewar takardar, za a gudanar da aikin ne a wani bikin da shugaba Buhari zai jagoranta, a fadar shugaban kasa a ranar Alhamis.
‘Yan kasashen ketare da suka ci gajiyar ba da takardar shaidar zama ‘yan Najeriya sun hada da ‘yan kasar Lebanon 108, ‘yan Italiya 16, ‘yan Burtaniya 14, ‘yan Nijar biyar, da kuma ‘yan Chadi biyu.
Har ila yau, an haɗa da shaidan zama ‘dan ƙasan ga wasu uan Masar, Amurka, Sudan, Sri Lanka, Siriya, Girka, Indiya, Jamhuriyar Dominican, Faransa, Palestine, Australia, Jordan, Cyprus, da Ireland.
An kuma lissafa sauran yan kasashen waje kamar haka: Serbia, Kenya, Belarus, Somalia, Ukraine da Habasha , da dai sauransu.
A WANI LABARIN KUMA: Murabus Ɗin Iyorchia Ayu Babbar Annoba Ce Ga Jam’iyyar PDP – Aniagwu
Mai magana da yawun kungiyar yakin neman zaben Atiku Abubakar, Charles Aniagwu, ya ce korar shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Dakta Iyiorcha Ayu, zai jefa babbar jam’iyyar adawa cikin rudani, gabanin zaben 2023 mai zuwa.
Aniagwu ya bayyana hakan ne a ranar Asabar a wani shirin gidan Talabijin a garin Asaba yayin da yake bayar da dalilan da suka sa jam’iyyar PDP ta binciko wasu hanyoyin da za a bi domin warware rikicin da take ciki