Hukumar EFCC ta bayyana cewa cikin watanni takwas sun yi nasarar gurfanar da mutum 33 bayan sun yi nasarar cafke mutum 293 da ake zargi da laifuka sama da 465, inda yanzu haka ya ce hukumar ke ci gaba da bincikensu.
Hukumar ta EFCC din ta ce har wala yau cikin wata takwas ta yi nasarar kwato kudi har naira miliyan 423. Shugaban EFCC din reshen Abuja, Aminu Aliyu shi ne ya bayyana hakan a ranar Talata, inda ya ce daga watan Janairun shekarar nan zuwa watan Agusta sun yi nasarar kwato Dala 39, 253 da kuma Yuro 2, 3330.
Aliyu ya tabbatar da cewa sashe na 6 na dokokin EFCC din shi ne ya ba su wannan damar na dakile cin hanci da rashawa tare da kwace kudin. Ya ci gaba da cewa; a karkashin shugabancinsa, za su tabbatar hukumar ta cimma nasarar kafa ta wajen ganin sun kawo karshen rashawa.
Ya ce kame 90 da suka yi sun yi shi ne sakamakon bayanan sirri da suka samu, a yayin da mutum 21 da aka gurfanar sashen lura da aikata laifuka ta Intanet ne suka gudanar da shi, sai kuma kame 110 da har yanzu ake ci gaba da bincikensa.
A wani bayanin na sa, ya tabbatar da cewa sun kama mutum biyu cikin jerin sunaye 77 da FBI suka fitar suna nemansu ruwa a jallo bisa zargin aikata damafar Intanet. Aliyu ya ce rashawa ba karamin gurbata al’umma yake yi ba, inda ya yi kira ga masu ruwa da tsaki da su tallafa wajen ganin an yaki cin hanci da rashawa.