Gwamnatin Tarayyar Kasar Habasha ta bayyana cewa, ta farmaki mayakan Tigray da zaune a yankin Afar, inda Kuma ta ikirarin cewa, ta yi nasaran fatattakan su daga yankin baki daya.
Sai dai Mayakan Tigray sun musanta wannan ikirarin da gwamnatin Kasar Habasha ta yi.
Mayakan sun ce “Mun tura dakarun mu ne zuwa yankin Amhara, saboda babu sauran wani fada a yankin Afar.”
KARANTA WANNAN LABARIN: Shugaba Buhari na ganawar sirri da Shuwagabannin Igbo a Imo
Idan za’a iya tunawa dai, A makonni da suka gabata, an gwabza kazamin fada a yankunan biyu, inda bangarorin biyu ke zargin junan su da keta hakkin dan-Adam.
Samun rahotanni mabanbanta tsakanin bangarorin biyu, ya sa kusan ba zai yiwu a tantance bayanai ba, game da yakin, wanda aka shafe kusan watanni goma sha daya, ana gwabza yaki tsakanin mayakan Tigray da na Gwamnatin Kasar Habasha.