Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya ce ‘yan kungiyar Boko Haram da su kayi saura a yankin Arewa maso Gabashin kasar nan ‘yan bindiga ne kawai, “kuma za mu ci gaba da daukan su a hakan.”
Shugaban kasar ya bayyana hakan ne yayin da ya karbi bakuncin Shugaban Kungiyar ICRC a fadar gwamnati da ke Abuja a ranar Talata.
Buhari ya jaddada cewa an ruguza kungiyar Boko Haram amma har yanzu akwai wasu mambobin kungiyar da su kayi saura da ke adabar mutane a Tafkin Chadi da kewaye.
“Haka ne yasa muke hadin gwiwa da Chadi, Kamaru, Jamhuriyar Nijar da sauran kasashe. Muna kuma amfani da sojojin saman mu kamar yadda ya kamata. ‘Yan ta’adda ne kuma za mu cigaba da daukan su a hakan,” a cewar shugaban kasar.
Shugaban kasar ya ce gwamnati ta mayar da hankali kan gyara kayayyakin gwamnati da suka lalace tare da tallafawa ‘yan gudun hijira da mutanen da suka rasa muhallansu saboda su koma gidajensu. Ya yabawa taimakon da ICRC da wasu kungiyoyi masu taimakon mutane inda ya jadada cewa gwamnati ba za tayi kasa a gwiwa ba wajen ganin an bawa dukkan mutanen tallafin da suke bukata.