• Tsohon Gwamnan jihar Zamfara ya ce “Mun gano wanda ke son rugujewar jam’iyyar APC”
• Abdul-Aziz Yari ya bayyana Sanata Ahmad Sani Yarima a matsayin Mai yi wa jam’iyar APC zagon kasa.
• ya Kuma ja hankalin jagororin jam’iyar da su kula da kudurin Yarima na kokarin ganin ya durkusar da jam Iyar.
Tsohon Gwamnan jihar Zamfara Alhaji Abdul-Aziz Yari ya bayyana cewa, lokacin da wasu manyan mutane goma 11 a jihar, suka kafa jam’iyar APC, Sanata Ahmad Sani Yarina ne ke yiwa jam’iyar zagwan kasa.
Lokacin da yake jawabi a taron masu ruwa da tsaki na jam’iyar da suka fito daga kananan hukumomin 4 na jihar, Yari ya ce, lokacin da aka kafa jam’iyar APC, Sanata Yarima ya nuna duna tantamar shi, tsakanin Jam’iyar ANPP da kuma Jam’iyar PDP.
“Lokacin da muke kokarin kafa jam’iyar APC, Ni da wasu yan jam’iyar ACN, CPC da kuma Gwamnonin ANPP, Sanata Yarima na kokarin durkusar da yunkurin mu” inji shi.
“Bari in kalubalanci Sanata Yarima ko ya dangwalawa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari kuri’a a zaben na shekarar 2019. Mai yasa zai sanya kanshi cikin jam’iyar da baya goyan bayan ta a lokacin zaben?”
KARANTA WANNAN LABARIN: NAF ta karyata rahoton hadarin jirgin Sama
Yari ya kara da cewa, a wanan yanayin da ake ciki na samun cigaba a siyasar jihar, ya kuma yi barazanar tuna asirin Sanata Yarima ga al’uma, domin su san asalin tsohon Sanatan.
Kazalika ya kuma ja hankalin jagororin jam’iyar APC dake jihar ta Zamfara, da su kala matuka da lamurorin Sanata Yarima, bisa yunkurin shi na ruguza jam’iyar ta hanyar amfani da manakisa.