Ma’aikatar harkokin aikin Gona ta tarayya ta tabbatar da cewa ta bada kwangilar ginin masallaci da kudinta ta kai naira miliyan talatin a Jihar Borno.
Sai dai Ma’aikatar ta ce ginin masallacin ya biyo bayan bukata ce da wasu yan gudun hijiran da rikicin Boko Haram ya koresu suka mika.
Wata sanarqa dauke da sanya hannun Daraktan Watsa Labaran Ma’aikatar ta ce baya ga masallacin, ma’aikatar za kuma ta samar da ruwan Famfo mai amfani da hasken rana da sauran wasu Kayyakin more rayuwa.
“Bari mu warware muku zare da abawa, gaskiya ne ma’aikatar ta bada kwangilar masallaci wa al’ummar da Boko Haram suka kora daga muhallinsu, yanzu haka sun yi sansani ne a karamar hukumar Ngarannam/Mafa a Jihar Borno” Cewar sanarwar.