Ƙungiyar tabbatar da aminci da kyautata ayyuka a jihar Kano ta goyi bayan gwamnatin Kano a kan yunƙurinta na samar da titin jirgin ƙasa.
Bayanin hakan ya fito ne ta cikin sanarwar bayan taro mai ɗauke da sa hannun shugaban ƙungiyar Farfesa Abdu Salihi da sakataren ƙungiyar Dakta Garba Shehu bayan kammala wani taro na yini guda da ƙungiyar ta shirya wa ƙwararru wanda aka tattauna game da aikin titin jirgin.
Sanarwar ta nuna cewa yunƙurin da gwamnatin Kano ta yi na wannan aiki abu ne mai kyau da zai taimaka wa harkokin sufuri, wanda bai kamata a ce an bar Kano a baya ba wajen ayyukan ci gaba ba.
Haka kuma yayin da yake zantawa da manema labarai game da taron Farfesa Salihi ya ce, sun shirya taron ne domin fahimtar amfanin al’amarin da kuma duba ribar da aikin zai haifar ga al’ummar Kano tare da duba yiwuwar gwamnatin ta ci gaba ko akasin haka.
Har wa yau, sanarwar ta shawarci gwamnatin Kano da ta yi amfani da tsarin haɗin gwiwa da ‘yan kasuwa masu zaman kansu yayin gudanar da aikin sannan ƙungiyar ta yabawa gwamna Dakta Abdullahi Umar Ganduje akan tsayawa wajen tabbatar da aikin tare da kira ga mutane da su daina sanya siyasa a kan yunƙurin ayyukan ci gaban jihar da ake gudanarwa.