Gwamnatin tarayya a ranar Litinin ta ce Najeriya ta samu gagarumin ci gaba, fiye da na shekarar 2015 lokacin da jam’iyyar PDP ke mulki. Kamar yadda Daily Post ta ruwaito.
Lai Mohammed, ministan yada labarai da al’adu ne ya bayyana hakan a lokacin da ya gabatar da shirin gidan talabijin na Najeriya NTA kai tsaye mai suna “Good Morning Nigeria”
KARANTA WANNAN LABARIN: Zamba: Kotu Ta Amince da Belin Ɗan Uwan Gwamnan APC da Wasu Kan N2bn
Mohammed ya ce gwamnatin Buhari ta cika burin ‘yan Najeriya idan aka yi la’akari da lokaci da yanayi.
Da yake magana kan nasarorin da gwamnatin ta samu, Mohammed ya ce a shekarar 2015, daukacin yankin Arewa maso Gabas ba sa cikin kwanciyar hankali kuma kananan hukumomi ashirin daga cikin ashirin da bakwai na jihar Borno suna karkashin mamayar mayakan Boko Haram.
Ministan ya ce a halin yanzu babu wani yanki na Najeriya da ke karkashin mamayar Boko Haram.
Ya kara da cewa, a shekarar 2015, kasar nan ita ce ta daya a kan shigo da shinkafa daga kasar Thailand amma tare da manufofi da tsare-tsare na gwamnati kan aikin noma, Najeriya na dogaro da kanta a bangaren abinci gaba daya.
A cewarsa, an baiwa miliyoyin manoma dama da tallafu a shirin Anchor Borrowers Programme yayin da kuma yawan masana’antun shinkafa a Najeriya ya karu daga biyu a shekarar 2015 zuwa 60 a halin yanzu.
Mohammed ya ce ana ciyar da yara miliyan goma a kullum yayin da gidaje miliyan biyu ke cin gajiyar shirye-shiryen gwamnati na kawar da talauci, Canjin Kudi, da dai sauransu.
Ya ce, “Mun kammala babbar hanyar Legas zuwa Ibadan da kuma gadar Neja ta biyu, wadda ta yi kaurin suna fiye da shekaru talatin.
“Duk da wannan zagon kasa, a yau mun yi aiki, titin jirgin kasa daga Legas zuwa Ibadan, titin jirgin kasa daga Abuja zuwa Kaduna da layin dogo na Ajaokuta zuwa Warri wadanda ba bu su kafin zuwanmu.”inji shi.
A wani labari kuma, Karancin Kudi: Masu Zanga-Zanga Sun Lalata Bankuna Biyu A Wata Jiha
Akalla bankuna biyu na kasuwanci a garin Ijoku da ke yankin Sagamu a jihar Ogun sun lalace sakamakon zanga-zangar da aka yisaboda karancin kudin Naira.
DAILY POST ta samu labarin cewa masu zanga-zangar da tun farko suka taru a kofar fadar Akarigbo na Remoland, Oba Babatunde Ajayi, sun kafa shingaye a kan manyan tituna wanda hakan ya kawo cikas ga zirga-zirgar ababen hawa.