tambuwal

Mun Kai Wa Wike Ziyara Ne Bisa Kokarin Ayyukan Raya Kasa- Gwamna Tambuwal

Gwamnan jihar Sakkwato, Aminu Waziri Tambuwal, ya bayyana cewa gwamnonin jam’iyyar PDP guda shida sun kaiwa gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike ziyara ta musamman ne don su yaba masa bisa namijin kokarin da ya ke yi wajen aiwatar da ayyukan raya kasa a cikin jiharsa ta Ribas.

Tambuwal ya ci gaba da cewa, gwamnonin sun karfafawa Wike guiwa tare da jan hankalinsa kan ya ci gaba da gudanar da irin wadannan ayyuka da ya ke yi don ci gaban jihar Ribas.

Tambuwal ya yi wannan bayani ne a fadar gwamnatin jihar Ribas da ke a birnin Fatakwal bayan sun gama tattaunawa da yammacin ranar Juma’a.

Gwamnonin da suka ziyarci Wike sun hada da: Gwamnan jihar Adamawa, Umaru Fintiri, gwamnan jihar Imo, Emeka Ihedioha, gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, gwamnan jihar Binuwe, Samuel Ortom da kuma gwamnan jihar Zamfara, Muhammad Bello Matawalle.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *