Hukumar yaki da cin hanici da yi wa tattalin arzikin kasa ta’annati a Nijeriya wato EFCC ta ce ta cafke wani mutum da yake sojan-gona a matsayin shugaban hukumar wato Ibrahim Magu.
Hukumar ta bayyana hakan ne a sanarwar da ta wallafa a shafinta dake Twitter, inda ta ce ofishin hukumar na garin Fatakwal ne ya cafke “Ibrahim Magu” a ranar Laraba.
Hukumar EFCC din ta ce wanda aka kama; “Yana amfani da sunan ne wajen zambatar jama’a tare da bata sunan wasu manyan jami’an hukumar raya yankin Neja Delta ta NNDC,” in ji EFCC.