Dakarun sojin Mozambique sun ce sun kama wani jagoran masu ikirarin jihadi dan kasar Tanzaniya a gundumar Nangade da ke lardin Cabo Delgado da ke arewacin kasar.
An kama shugaban ne mai shekaru 39, wanda aka fi sani da Ali, tare da wasu mahara shida masu alaka da kungiyar IS, in ji jami’an sojin.
Rahotanni sun bayyana cewa, ya kasance daya daga cikin shugabannin mayakan da aikinsu shi ne daukar sabbin mayaka da kuma kai hare-hare.
Kame shi dai na zuwa ne a daidai lokacin da yanayin tsaro ke kara tabarbarewa a gundumar, inda a ‘yan kwanakin nan ake kai samun hare-haren masu jihadi.
A cikin kimanin makonni biyu, maharan sun kai hari a kauyuka bakwai a Nangade, kamar yadda kafafen yada labaran kasar suka ruwaito.
Harin na baya-bayan nan ya faru ne a kauyen Limualamuala a ranar Asabar din da ta gabata kuma ya yi sanadin mutuwar mutane shida, yayin da suka halarci Wani biki.