Majalisar masana harhada magunguna ta Najeriya (PCN) ta ce ta rufe haramtattun shagunan shan magani guda 358 a babban birnin tarayya Abuja tsakanin ranakun Litinin da Alhamis na wannan mako.
Magatakardar majalisar, Pharmacist Ibrahim Babashehu Ahmed ne ya bayyana hakan jiya a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Abuja.
Ya ce an rufe shagunan sayar da magunguna 90 da shagunan sayar da wasu 268 daga cikin jimillar 584 da aka ziyarta a yayin gudanar da aikin.
Ya ce an kulle su ne bisa laifuka daban-daban kamar yin aiki ba tare da yin rajista da hukumar PCN ba, rashin sabunta lasisin wuraren zama, rarraba kayayyakin da suka dace ba tare da sa ido kan magunguna ba, rashin wurin ajiya mai kyau da tsaftar muhalli da dai sauransu; yayin da aka ba wa shagunan sai da magunguna biyar lasisin haƙƙin mallaka.
Ahmed ya ce an kama wasu masu sayar da magunguna hudu, inda ya kara da cewa, “An kama uku daga cikin su da laifin karya PCN, daya kuma da laifin nuna lasisin sayar da magunguna na bogi a shagonsa.
Comments 1