Mun sami Layoyi da manyan Makamai a gidan Sunday Iboho, Hukumar DSS
A wani takaitaccen labari da Jami’an sirri suka sanar a daren jiya Alhamis sun ce ” A hanlin yanzu dai Sunday Iboho ya ari ta Kare”
KARANTA:-An yanke wa wani Matashi hukuncin shekara biyu gidan Kaso
Jami’an tsaro na sirri sun ce, sun kai samame a Unguwar da Sunday Iboho mai fafutukar kafa kasar Oduduwa, ke zaune a garin Ibadan babban birnin Oyo.
Peter Afunanya mai magana da yawun jami’an tsaro na sirri ya ce ” munyi nasarar cafke mutane Sha biyu dake goyon bayan Sunday Iboho a lokacin da muka kai samame. Kamar yadda Jaridar Dailytrust ta wallafa.
Ya kuma gabatar da Layu, Bindigu, Fasfo da wayar Tarho duk abubuwan da suka tarar a cikin gidan.
Ga hotunan kamar haka: