Paul Pogba ya bukaci abokan wasansa a kungiyarsa ta Manchester United da su sha kuruminsu gabanin babban wasa tsakaninsu da Liverpool a ranar Lahadi.
United ke jan ragamar gasar Firimiyar Ingila a wannan lokaci, a karon farko tunda suka lashe gasar a kakar wasan shekarar 2012 -13, kuma su na iya bada tazarar maki 6 idan suka doke Livcerpool a Anfield
Pogba ya shaida wa manema labarai cewa wasan zai kasance mai armashi, yana mai kira ga abokansa a United da su shirya sosai duba da cewa babban wasa ne.
Pogba ne ya ci kwallon da ta bai wa United nasara a fafatawarsu da Burnley, hakan ya dawo da tawagar Ole Gunnar Solskjaer cikin hayyacinta.
Yanzu Manchester United ta buga wasanni 15 a gasar Firimiya ba tare da an doke ta ba, kuma cikin su ta lashe 12.