Mun shiryawa Yan kwadago, Elrufai
Gwamnan Jahar Kaduna Malam Nasiru Elrufai, yace shirye muke tsaf dangane da yunkurin daukan mataki da Yan kwadago ke niyyar yi a Jahar ta Kaduna.
Gwamna Elrufai yace a lokacin da suke zantawa tare da manema labarai na gidan talabijin na BBC, ya cire Yaronsa daga makarantar gwamnati saboda rade-raden da akeyi Yan bindiga zasu dauke shi.
KARANTA:-Baka da hannu wajan yakin neman zaben mu, Yan majalisu ga Lai Muhammad
Gwamnan ya nuna alhininsa kan sake zanga-zangar da Yan kwadago keyi karo na biyu. Ya zargin Yan kwadagon kan karyar da sukeyi suna zanga-zangar ne saboda an kori ma’aikata.
Kamar yadda ya ambata “Kananan Hukumomi wanda suke cin gashin kansu, sun sallami ma’aikatan su da dama, saboda suna fuskantar rikicin kan kudade sama da gwamnatin Jahar, in da suka sallami ma’aikata akalla 2,000 wa’inda mafiya yawansu basu can-can ta ba wasu kuma takardunsu na boge ne, da dai sauran dalilai.”
“Kungiyar Yan kwadagon na Shirin dawowa, to muna shirye da hakan, iyakar abunda zamu ce kenan, ba za mu basu damar cutar da rayuwar Mutanen Kaduna ba, munyi shiri tsaf akan haka.”