Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa a ranar Talata ta ce za a fara samar da sabbin katunan zabe na dindindin a cikin watan Nuwamba mai zuwa. Kamar yadda Channels TV ta ruwaito
Shugaban hukumar ta INEC Farfesa Mahmoud Yakubu ya bayyana haka ne a wajen wani taron bayar da gudunmawa ga dorewar dimokuradiyya a birnin Washington DC na kasar Amurka.
KARANTA WANNAN LABARIN: Tsadar Man Fetur: Wasu Tsirarun Mutane Sun Jefa Rayuwar Mu Cikin Wani Hali—- Al’umar Zamfara
A nasa jawabin, Shugaban INEC, Farfesa Mahmoud Yakubu, ya ce an samu mutum biyu miliyan 2.7 da suka yi rajista sau biyu, daga cikin wadanda za su kada kuri’a da hukumar ta tantamce a baya.
A cewarsa, kusan kashi 50 cikin dari na sabbin masu katin rajistar zabe an kammala su, amma har yanzu ba a raba su zuwa cibiyoyin tattara sakamakon zabe ba.
Ya kuma nuna damuwarsa game da karuwar rashin tsaro a fadin kasar, yana mai cewa hukumar na cikin zullumi
Ya kuma kara da cewa, hukumar na sa ido, musamman a yankin Arewa maso Yamma da kuma Kudu maso Gabashin kasar nan.
Yakubu, wanda ya ce, ‘yan Adam ne ke gudanar da zabe, ya cigaba da cewa, hukumar ta damu da tsaron jami’anta, da kayan aiki, da ma su kansu masu kada kuri’a.
Kazalika Shugaban na INEC ya ce, , idan ba wadannan abubuwan da aka ambata ba, ba za a iya gudanar da zaben ba yadda ya kamata
Shugaban hukumar zaben mai zaman kanta ta kasa ya kuma ce masu ruwa da tsaki “sun yi magana da jami’an tsaro kuma sun ba su tabbacin cewa al’amura za su daidaita kafin zaben na shekarar 2023 mai zuwa..
A WANI LABARIN KUMA: Al’ummar Tukuntawa Sun Godewa Ganduje Bisa Basu Kyautar Filaye
Al’ummar unguwar Tukuntawa dake karamar hukumar birni sun yabawa gwamnan jihar Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje sakamakon wasu filaye da gwamnan ya baiwa al’ummar unguwar cikin rukunin filayen da aka yanka a gidan radio manoma.
Taron dai an shirya taron ne bisa jagorancin mai unguwar Malam Nuhu Garba.