Shugaban kasa Muhammadu Buhari a yayin da yake yiwa ‘yan kasa jawabi a ranar Talata a ranar tunawa da ‘yancin kai, ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ta tara biliyoyin nairori cikin shekara hudu ta hanyar kaddamar da shirin tattara bayanan jami’ai wuri guda wato IPPIS a takaice.
Sannan ya tabbatar da cewa ta wannan hanyar sun yi nasarar dakile satar kudaden al’umma da karkatar da su. Haka zalika ya ce amfani da asusun bai daya na TSA da kuma tsarin fallasa ya taimaka wajen rage cin hanci da rashawa a tsakanin ma’aikata.