Gwamnan Jihar Katsina Alhaji Aminu Bello Masari ya bayyana cewa lokaci ya wuce da Jahohi zasu dogara Kachokam, akan kason kudaden mai da ake samu daga Gwamnatin Tarayya.
Gwamna Masari na magana ne a lokacinda yake bude taron Tsare-Tsaren kawo cigaban Jihar Katsina nan da shekaru 10 masu zuwa, wanda ya gudana a dakin taro na Hukumar Kula Da Ma’aikatan Kananan Hukumomi ta Jiha.
Taron Kungiyar Ceto Jihar Katsina wato “Save Katsina Group”ce ta shiryashi, inda ya samu halartar masu ruwa da tsaki daga bangarori daban-daban na kasarnan, kamar yadda majiyar Jaridar Dimokuradiyya ta ruwaita.
KARANTA WANNAN LABARIN:
Taron nada manufar tattauna shawarwari da gudummuwar masu ruwa da tsaki, da zata samar da wani kundi Wanda za’ayi amfani da shi ta fuskar tafiyar da Jihar Katsina, domin samun cigaba mai dorewa nan da shekaru 10 masu zuwa.
A jawabinsa, Gwamna Aminu Bello Masari ya yabawa kungiyar akan shirya taron, wanda ya bayyana a matsayin abinda zai taimaka wurin dawo da matasa cikin hayyacinsu akan su nisanta da jiran aikin Gwamnati.
Gwamnan yace daga cikin Kudi kimanin naira biliyan 6 da Jihar Katsina Ke samu, ana amfani da sama da naira biliyan 5 wurin biyan albashi da alawus-alawus na ma’aikatan Jihar.
A sabili da haka a halin yanzu Gwamnati bata iya samar da aiki ga kowa da kowa, sai dai maimakon hakan akwai bukatar matasa da suka kammala makarantu su tsunduma a cikin sana’oi maimakon jiran aikin Gwamnati.
A sa’ilinda yake bada tabbacin yin amfani da kundinda za’a fito da shi bayan taron, Gwamna Masari yayi fatan cewa za’a bada shawarwari da zasu kawo cigaban jiharnan.
A nashi jawabin, Shugaban taro kuma Galadiman Katsina Hakimin Malumfashi Mai Shari’a Sadiq Abdullahi Mahuta, yace taron ko shakka babu zai bayar da gudummuwa ta fuskar kawo cigaban Jihar Katsina.
Shugaban Kungiyar ta Save Katsina Group Kwamarad Hamza Umar Saulawa, yace taron zai mayar da hankali akan inganta tafiyar da Shugabanci da Tattalin arziki da sauran batutuwa da suka shafi cigaban al’umma.