Gwamnatin jihar Sakkwato ta yi wa ma’aikatan boge dubu 8 da masu karbar albashin da bai dace ba afuwa.
Kamfanin dillancin labaran Nijeriya ya labarto cewa; Kwamishinan kudi na jihar Alhaji Abdussamad Dasuki ne ya bayyana hakan a wani taron manema.
Ya ce an yi hakan ne don ma’aikatan gwamnatin da suke karbar albashin da ba halalinsu ba ko suke abubuwan da ba su dace ba da su samu kwarin gwiwar bayyana kansu ga gwamnati ba tare da al’umma sun sani ba don samun afuwar gwamnati.
Za a rufe karbar afuwar ne a ranar 9 ga watan Disambar 2019.