Daga wakilin Dimukaradiyya Mukhtar Yakubu Kano.
Daya daga cikin masu shirya fim da suka dade ana damawa da su a masana’antar fina-finai ta Kannywood Auwal Uba Kwakwatawa ya bayyana sauyin da aka samu a cikin masana’antar da cewar, wani al’amari daga Allah wanda in dai ka yarda da shi ka san komai na iya faruwa a kowanne lokaci.
Auwal Uba Kwakwatawa ya bayyana hakan ne a lokacin tattaunawar su da wakilin Jaridar Dimukaradiyya a kan yadda aka samu sauyi a cikin masana’antar.
In da ya ke cewa “Mu mun yarda harkar fim har yanzu sana’a ce don haka duk da a yanzu kasuwar da za a buga CD a kai ta mutu muna yin wanda za mu kai gidajen TV mu sayar musu ko kuma wanda za mu dora a kan You Tube, to ka ga wannan duk harka ce ta ci gaba don haka a yanzu idan na yi aiki sai na dora a ka. You Tube Dina ko kuma na sayarwa wasu su dora a na su. Kuma gaskiya jama’a sun karbi harkar You Tube sosai, domin idan har ka yi mai kyau to mutane za su bi su kalla, amma saboda wasu ba sa dora fim nagari sai ka ga daga sun fara sai su watsar don mutane suna da hankali sai abu mai kyau so ke kalla.don haka wasu daga sun fara sai su watsar saboda babu abin da za su saka. ” Inji shi.
KARANTA WANNAN LABARIN: Yan sanda sun Cafke Masu Garkuwa, yayin da suke Amsan kudin Fansa a Ogun
Mun tambaye shi ko wacce matsala su ke fuskanta su masu dora fim a YouTube?
Sai ya ce” wato matsalar da mu ke fuskanta ita masu satar mana kaya su dora a kan na su You Tube din, sai ka ga mutam bai san yadda aka yi ka samar da aikin ka ba Amma kafin ka dora sai su sata su Dore a nasu kuma wannan zallar haramun ne. Don haka duk wanda ya yi mana haka to wallahi ba mu yafe masa ba. ” A cewar shi.
Daga karshe ya yi kira ga abokan sana’ar sa da su ji tsoron Allah wajen gudanar da Sana’ar su.