Darkta-Janar na Hukumar Kula da bada shaidar katin zama ɗan ƙasa ta Nigeria Abubakar Aziz, ya bayyana cewar hukumar na aiki tuƙuru domin ganin ta yiwa duk ƴan Nigeria rajistar katin zama ɗan ƙasa a shekarar 2022.
Ya bada tabbacin cewa NIMC zata ƙirƙiri wani tsari dazai taimaka wajen ɗaukar hoton kowane ɗan Nigeria da dukkanin bayanai dazasu taimaka wajen aikin.
Majiyar Jaridar Dimokuraɗiyyar ta ruwaito cewar, Hukumar NIMC a halin yanzu ta yiwa ƴan Najeriya miliyan 60,d da akwai da yawan ƴan ƙasar da suke ta nuna damuwa, akan rashin saurin rashin rajistar wanda hukumar ke yi.
KARANTA WANNAN LABARIN: Apapa: An Baiwa Direbobin Manyan Motoci Wa’adin Kwanaki 7
Amma a jawabin shi a lokacin da ya kai ziyara ga shugaban Hukumar hana zagon ƙasa Abdulrasheed Bawa, a Abuja a ranar Alhamis, Aziz yace “muna so mu sanar da shugaba akan cigaban da aka samu a ɓangaren tattalin arziki musamman wajen samar da bayanan da zasu fallasa masu damfara a yanar gizo.
“Muna aiki tuƙuru domin yiwa ƴan Najeriya rajista ya zuwa shekara mai zuwa, muna bada tabbacin bada goyon baya da aiki a tare da kai,”inji shi.
A cewar jawabin da mai magana da yawun Hukumar Kula da bada shaidar ɗan ƙasa Wilson Uwujaren ya fitar, ya bayyana cewar Bawa shugaban EFFC ya bada tabbacin aiki da NIMC wajen tabbatar dacewa Nigeria nada wasu kundin bayanai dazai taimaka wajen yaƙi da masu yiwa tattalin arziki zagon ƙasa.
Dayake bayyana irin matsayin NIMC wajen kasancewar ta ƴar uwa abokiyar tafiya, Bawa ya bayyana irin mahimmancin rajistar katin ɗan ƙasa ga hukumomin tsaro.