Jaruman shirin Dadin Kowa Hassana Yusuf da Hussaina Yusuf wadanda aka fi sani da’ yan biyun Shirin Dadin Kowa sun bayyana aniyar su ta yin aure a nan gaba kadan.
Jaruman su bayyana Hakan ne a lokacin tattaunawar su da Dimukaradiyya in da su ke cewa.
“Mu a yanzu babban burin mu shi ne nan gaba kadan mu yi aure wannan shi ne abin da ya rage a gare mu domin duk wani suna da a ke yi a cikin harkar fim mun riga mun yi”.
KARANTA WANNAN LABARIN: Shugaban Somaliya Ya Dakatar Da Firaministan Kasar Yayin Da Rikicin Zaben Ke Kara Ta’azzara
Da muka tambaye su ko Don ba sa cikin Dadin Kowa ne a yanzu shi ya sa suka ga abu mafi alheri a gare su su yi aure?
Sai suka ce “Ai ko muna cikin shirin ma muna sa ran mu yi aure, Allah ne bai kawo ba a lokacin Amma tun tuni muka so mu yi auren, Kuma har yanzu muna da shirin. Kuma maganar Dadin Kowa, ai shiri ne daman mun San nan gaba komai dadewa aikin mu zai Kare a ciki, Amma mun san rayuwar aure ita ce ba ta karewa a wajen ‘ya Mace, don haka mu ke fatan Allah ya kawo mana mazaje nagari da za su aure mu. ”
Daga karshe sun yi Kira ga masoyan su da su taya su addu’a domin su samu maza masu tsoron Allah da za su rike su cikin mutunci da kulawa.
Comments 1