Hukumar shirya jarabawar share fagen shiga jami’o’i ta kasa JAMB ta ce Akalla Dalibai Milliyan Daya ne da dubu Dari hudu suka zauna rubuta jarabawar na wannan shekarar ta 2022 a fadin kasar nan, ta na Mai cewa Nan ba da jimawa ba za ta saki sakamakon su.
Hukumar ta bayyana hakan ne a wani sakon mako-mako da ta rabawa manema labarai a Ofishin magatakaddar ta dake Abuja a yau talata.
Kana JAMB ta ce nan ba da jimawa ba zata saki sakamakon jarabawar wadanda suke rubuta jarabawar da zarar ta kammala tantance su.
Sanarwar ta yi nuni da cewa, hukumar na sake duba na’urar daukar bayanan sirri wato CCTV a yayin da zaman rubuta jarabawar, inda ta ce, duk dalibin da takama da magudin jarabawar zata soke sakamakon shi daga bisani.
A wani labari Kuma na daban.
Mamakon Ruwan Sama Da Tsawa Sunyi Sanadiyyar Mutuwar Mutane 5 Tare Da Jikkata 41 A Damaturu
Akalla mutane biyar ne aka tabbatar da mutuwarsu, yayin da wasu 41 suka samu raunuka daban-daban a ranar Litinin din da ta gabata, yanzu haka ana kwantar da su a Asibitin kwararru da ke Damaturu Jihar Yobe sakamakon mamakon ruwan sama da kuma tsawa.
Babban Sakataren Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Yobe (SEMA) Dokta Mohammed Goje ya tabbatar da faruwar lamarin ga wakilinmu a Damaturu a ranar Talata.
A cewar sa “SEMA ta mayar da martani ga wadanda ginin ya rufta saboda tsananin iska da ruwan sama da aka asamu”.
“Tawagar bincike da aikin ceto ta Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Yobe SEMA a ranar 9 ga watan Mayu, 2022 ta amsa kiran gaggawa daga al’umomin yankin da abin ya shafa.
Hukumar tace ta aike da tawagar jami’an ta don tallafawa wajen kwashe wadanda abin ya shafa zuwa asibitin kwararru na jihar Yobe.”
Goje ya bayyana cewa “jimillar wadanda abin ya shafa 41 sun fito ne daga al’ummomi/da yan kuna daban-daban guda 6.
A cewar sa yankunan sun hada, Waziri Ibrahim, unguwar Abbari, NayiNawa, Pompomari, Sai rukunin gidajen ‘yan majalissu, kan titin Gujba da kuma Maisandari.
Kazalika yace abin takaici mutane 5 sun mutu maza 2, mace babba 1, da kuma ‘yan mata guda 2.