Ministan kula da harkokin cikin gida, Rauf Aregbesola, ya ba da tabbacin cewa za a kammala gidajen gyaran hali da zai ci mutane 9,000 a jihohi uku na kasar nan zuwa nan da watan Disamba, 2022.
Gidajen Gyaran halin da kowannensu zai ci mutane 3,000 an samar da su ne a Jihohin Kano, Ribas da Abuja.
Aregbesola, wanda ya bayyana hakan ga manema labarai bayan wani rangadi da ya kai cibiyar kula da gyaran halin ta Karshi, dake Abuja, mai daukar mutane 3,000, ya ce bayan kammala ayyukan, za a kwashe fursunonin da basu cancanci zama a inda suke ba, domin mayar da su can.
KARANTA ANAN: An Ceto Mutane Tara A Yayin Da Ruwa Ya Rushe Gini A Legas
Da yake bayyana matakin kammala kowane ginin, Aregbesola ya ce an kusa kammala aikin a Kano yayin da kayayyakin da ke Rivers da Abuja ke kan kammala d kusan kashi 55%.
Ya ce “Buri na shi ne a samu guda uku na farko daga cikin ayyuka shida da za a kammala kafin wannan gwamnati ta kare.
“Zan tuntubi shugaban kasa domin tallafa wa aikin a Kano, Ribas da Abuja. wanda hakan zai bayar da gudunmawar ganin an kammala aikin cikin nasara.
Muna da ware kowane gida zuwa sashi sashi domin ajiye kowa a inda ta cancanta,” inji shi.
A wani labarin kuma: An Hana Gidajen Talabijin Din Kenya Yada Shirin Rantsar Da Ruto
A dai dai lokacin da ake shiryen-shiryen biki mika mulki ga sabuwar gwamnati tawagar zababben shugaban kasar Kenya, ta hana kafafen yada labaran cikin gida yada bikin rantsar da sabon shugaban kasar, tare da ba da haƙƙin watsa shirye-shirye na musamman ga Multichoice Kenya Limited, Gammayyar ƙungiyar rukunin kafafen talbijin dake da asali daga Afirka ta Kudu.
Sai dai kungiyar ma’aikata kafafen yada labarai na kasar Kenya wago KBC, bai da wani karfi a kungiyar ta Multichoice Kenya Limited.