Jam’iyyar PDP a ranar Juma’a ta taya Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike murnar nasarar da ya samu a kotun koli bisa tabbatar da shi a matsayin zababben gwamnan jihar Ribas a zaben da ya gabata.
Jam’iyyar ta bayyana hakan ne a wata sanarwa da Sakataren yada labaran jam’iyyar, Kola Ologbondiyan, ya fitar, inda ya bayyana hukuncin kotun a matsayin nasarar da adalci ya yi, kuma aka tabbatar da zabin al’umma bisa masu son yiwa dimokradiyya zagon kasa a cewarsa.
Ologbondiyan ya kara da cewa hukuncin kotun ya sake karfafa fatan a’umma tare da kare mutuncin kotun koli. Sannana a cewarsa wannan ya yi nuni da yadda kotun koli ta shirya domin yiwa kowa adalci tare da kare dokokinta.