Shugaban Rikon Kungiyar Yarbawa ta Afenifere Pa Ayo Adebanjo ya ce kungiyar ba wai ta kafe kan cewa sai Fulani sun bar yankin Yarbawa ba.
Ya ce Ƙungiyar tana magana ne kawai kan korar gurbatattu daga cikin su da su tattatar su kama gaban su.
Pa Adebanjo ya bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya yi wa Allah ya yi wa Annanbi a sake wa kasar nan fasali, domin ta hakan nen kawai za a kawo karshe duk wasu matsaloli da suka yi wa kasar nan daurin huhun goro.
Shugaban Kungiyar yana wadannan maganganu ne yayin Jana’izar tsohon shugaban kungiyar Mista Yinka Odumakin da ta gudana a jihar Oshun a yau Asabar
Shugaban Afeniferen ya ce muddun ba wai an sake fasalin kasar ba ne, to lallai haka za ta ci gaba da tafiya ba tare da an gane gaban ta an gane baya ba, don haka ne ya sa suka kafe lallai sai an dauki matakin hakan.