Kungiyar Malaman Kwalejijojin Kimiya da Fasaha ta Kasa ASUP ta ba gudu ba ja-da-baya dangane da yajin aikin da take yi a halin da ake ciki.
Kazalika Ƙungiyar ta nuna fushin ta kan yadda ake ci gaba da zaben shugabannin Kwalejijoji a kasar nan, a abinda ta kira mai uwa a gindin murhu.
Shugaban Kungiyar Anderson Ezeibe shine ya sanar da haka a wani taron gaggawa da Kungiyar ta shirya a Kwalejin Kimiyya da Fasaha na Gwamnatin Tarayya dake Auchi a Jihar Edo ya jinjina wa Malaman Kwalejijojin bisa nuna mubaya’ar su wa Ƙungiyar wajen shiga yajin aikin.
Daga nan sai ya yi Allah wadai bisa irin yadda ake nada shugabannin Kwalejijoji kimiyya da fasaha a kasar da ba su kware ba, domin a cewar shi gabannin zama shugaban kwaleji sai mutum ya kasance babban malami a kowane kwaleji na a kalla shekara.
Idan za a iya tunawa dai a ranar shida ga watan jiya ne dai Ƙungiyar ta tsunduma Yajin Aikin bisa rashin biya mata wasu bukatu kamar yadda ta bayyana.