Mai magana da yawun kungiyar yakin neman zaben Atiku Abubakar, Charles Aniagwu, ya ce korar shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Dakta Iyiorcha Ayu, zai jefa babbar jam’iyyar adawa cikin rudani, gabanin zaben 2023 mai zuwa.
Aniagwu ya bayyana hakan ne a ranar Asabar a wani shirin gidan Talabijin a garin Asaba yayin da yake bayar da dalilan da suka sa jam’iyyar PDP ta binciko wasu hanyoyin da za a bi domin warware rikicin da take ciki.
KARANTA ANAN: Wasu Daga Cikin Abubuwan da Zasu Faru Bayan Mutuwar Sarauniya Elizabeth II
A cewar Aniagwu, jam’iyyar PDP na sake duba batutuwan ne bisa abin da dokokin jam’iyyar suka halatta.
Ya ce shawarar cewa dole ne Ayu ya sauka daga karagar mulki ya biyo bayan kuri’ar amincewa da kwamitin zartarwa na kasa (NEC) ya yi, wanda ya bashi damar ci gaba da shugabancin, lamarin da bai yiwa wasu dadi ba.
A wani labarin kuma: Har Yanzu Boko Haram Na Rike Da Yan Matan Chibok 98 – Rundunar Soji
Har yanzu akwai yan matan makarantar Chibok 88 dake tsare wajen masu garkuwa da su, wato yan ta’addan Boko Haram.
Jaridar Dimokuraɗiyya ta rawaito cewa Adadin Yan Matana da Boko Haram suke sace ranar 14 ga watan Afrilun shekarar 2014, sun kasance 276, kuma sauran wasu sun tsira wasu kuma sun mutu.