Kungiyar kare hakkin Musulmi ta MURIC ta jinjinawa Gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai bisa sanya yaronsa a makarantar gwamnati kamar yadda ya yi alkawari.
Daraktan MURIC din, Farfesa Ishaq Akintola shi ne ya yi wannan jinjinar a wata sanarwa da ya sanyawa hannu a ranar Litinin. Inda ya ce halin da El-Rufai ya nuna abin a jinjina masa ne. Domin a cewar MURIC ya cancanci yabo.