Akalla mutane uku ne suka riga mu gidan gaskiya sakamakon wani hatsari da ya auku tsakanin tirela da wani mai mashin a titin Abiola dake Birnin Abekuta.
Kakakin Rundunar Hukumar Kiyaye dokokin hanya ta Jihar Ogun Mista Bababtunde Akinbiyi ya tabbatar da hakan wa manema labarai a yau asabar.
Cewar Kakakin rundunar lamarin ya faru ne yayin da wani mai babur yayi yunkurin wuce wata tirela inda babur din ya kwace mishi inda nan take tirelar ta murkushe direban babur din da Fasinjojin da yake duake da su har lahira.
Akinbiyi ya kuma ce al’amarin ya auku wuraren karfe takwas na dare ranar Juma’a inda direban tirelar ya murkushe su kuma nan take aka aika mamatan zuwa ma’adanar gawarwaki na asibitin Ijaye dake birnin Abekuta.
Daga bisani ya ja hankalin matuka ababen hawa da su yi wa allah su rika tuki cikin tsantsaini kana su rika bin dokokin hanya sua da kafa.