- Dan takarar gwamna na jam’iyyar NNPP a jihar Ebonyi Adol-Awam da tulin mambobin jam’iyyar sum koma APC.
- Daukar matakin sauya shekar zuwa jam’iyyar APC mai mulki ya biyo bayan dimbin rigingimun da suka dabaibaye jam’iyyar NNPP a jihar.
- Adol-Awam yace zai cigaba da jajircewa wajen ganin an samar da ci gaba da shugabanci na gari domin amfanin kowa.
Dan takarar gwamna na jam’iyyar New Nigeria Peoples Party NNPP a jihar Ebonyi, Prophet Chris Adol-Awam, ya koma jam’iyyar APC mai mulki a ranar Juma’a tare da wasu mambobin jam’iyyar 2,000,kamar yadda Daily Post ta rawaito.
Adol-Awam ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai jim kadan bayan wata ganawa da ‘yan jam’iyyar a gidansa da ke Abakaliki babban birnin jihar Ebonyi.
KARANTA WANNAN: Da Dumi-Dumi: An Sanya Ranar Gudanar da Zaben Kananan Hukumomi a Jihar Yobe
Adol-Awam ya sauya sheka ne tare da abokin takararsa da kuma mambobin jam’iyyar a sassan mazabun siyasa 171 da kananan hukumomi 13 na jihar.
Ya bayyana cewa sun yanke shawarar ruguza tsarin jam’iyyar NNPP zuwa jam’iyyar APC mai mulki ne saboda dimbin rigingimun da suka dabaibaye jam’iyyar a jihar.
A cewarsa: “Da kaushin zuciya ne na sanar da kawo karshen tafiyata tare da jam’iyyar NNPP. Bayan na yi nazari sosai da natsuwa, na yanke shawarar komawa jam’iyyar APC da nake ganin itace gidana na siyasa ta gaskiya.”
Da yake bayyana dalilin daukar matakin, Adol-Awam ya ce, “Kafin hadewar da ta hada jam’iyyun ACN, ANPP, CPC, da kuma bangaren APGA zuwa APC, na taka rawar gani wajen kawo jam’iyyar ACN jihar Ebonyi a shekarar 2010.
“Na samu damar zama dan takarar gwamna a jam’iyyar a zaben shekarar 2011. Haka kuma, na dauki nauyin daukacin ‘yan takarar Majalisar Wakilai 24 na jam’iyyar a wancan zaben kuma na ba da gudunmawa sosai wajen hadewar.
“Alkawarin da nake da shi na tabbatar da manufofin jam’iyyar APC a kodayaushe ba ya gushewa.
“Da wannan ne nake alfahari da sanar da cewa na dawo APC, jam’iyyar da nake kira gida. Ina tahowa da ni da ciyawar da aka kafa a kananan hukumomi 13 na jihar nan. Tare, za mu daidaita da gwamnatin hadin kan kasa don amfanin al’ummar Ebonyi.”
Ya kuma kara da cewa matakin da ya dauka na komawa jam’iyyar APC ya samo asali ne daga irin nauyin da ya rataya a wuyansa da kuma burinsa na yi wa jama’a hidima.
“Na ci gaba da jajircewa wajen ganin an samar da ci gaba da shugabanci na gari domin amfanin kowa.
“A tare, mu himmatu wajen gina jihar Ebonyi mai wadata da za mu yi alfahari da ita,” inji shi.
A wani labarin kuma, Tallafin Fetur: Za Mu Sake Duba Mafi Ƙarancin Albashi Don Yin Tunani Na Gaskiya — Tinubu
Shugaba Tinubu ya ce mafi karancin albashin ma’aikata na kasa na bukatar a sake duba na tsakani kan lamarin.
Inganta rayuwar ‘yan Nijeriya ya kasance babban abin da gwamnatina ta sa a gaba, tare da karin manufofin tattalin arziki da ya shafi jama’a.
Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnonin APC a karkashin inuwar kungiyar gwamnonin jam’iyyar PGF suka dora alhakin cire tallafin man fetur kan Tinubu.