A gasar musabakar karatun Alkur’ani da rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta shirya na kwanaki biyu ta sanar da jami’in da ya sami nasara bayan fafatawa a tsakanin jami’an na ta.
Gasar wadda ta kunshi duk jami’an da suke da mukamai, wanda ta rika yinsa mataki-mataki a tsakanin su daga mutum 60 aka fara zuwa mutum 40 haka aka ci gaba da gwabza gasar a tsakanin jami’ai.
Haka kuma an zo mutum 5 inda daga nan aka sake zubar da 3 suka zama mutum 2 wanda su ne suka yi gwabzawa ta karshe aka fitar da wanda ya sami nasara a tsakanin su mai mukamin DPO sunansa Mahi Ahmed Ali.
Mahi Ahmed Ali shi ne ya sami nasara kuma yana rike da ofishin hukumar da ke karamar hukumar Takai ta jihar Kano a gasar musabakar Karatun Alkur’ani mai girma wanda aka yi cikin kwanaki biyu ranar Laraba da Alhamis.
Jaridar Dimukuradiyya ta rawaito cewa an gudanar da taron ne a shelkwatar rundunar ‘yan sandan jihar Kano da ke Bamphai karkashin jagorancin Kwamishina CP Sama’ila Shu’aibu Dikko.
Wannan shi ne karon farko da rundunar ‘yan sanda ta Kano ta gudanar da irin wannan taro na karatun Alkur’ani mai girma a tsakanin jami’anta.