Al’ummar Musulman Jihar Kwara sun ba da shawarar sauya sunayen duk makarantun da suke mallakin Musulmai da Kirista a Jihar, a wani bangare na magance matsalar sanya hijabi ga yaya mata da taki ci taki cinyewa a Jihar.
Sun bayyana hakan ne a cikin wata wasika da suka aike wa Gwamnan Jihar, AbdulRahman AbdulRazaq, inda suka shawarar ce shi da ya dauki matakai guda shida wajen magance matsalar sanya hijabi ga dalibai mata musulmi ke yi a daukacin makarantun gwamnati na jihar.
da bukatun Makarantun, ya kamata Gwamnatin Jihar Kwara ta sauya sunayen duk makarantun da Musulmi da Kirista suke zuwa a baya, ta hanyar sanya ‘Gwamnati’ a cikin su, misali, Makarantar Sakandaren Gwamnati ta Ansarul Islam dake Ilorin,, Kwalejin Gwamnati ta Bishop Smith Memorial dake Ilorin,” kamar yadda al’ummar yankin suka bayyana a cikin wasikar.
Kwafin wasikar mai kwanan wata 7 ga watan Yuni shekarar 2022 mai lamba KWS/MS/01/22 dauke da sa hannun shugaban kungiyar Alhaji Ishaq AbdulKareem da Sakatarenta Farfesa Ibrahim Abikan, sun bai wa manema labarai a Ilorin babban birnin jihar a jiya Litinin.
Kungiyar musulman kuma bukaci a biya iyalan marigayi Habeeb Idris diyya da ake zargin an kashe a ranar 3 ga watan Fabrairun 2022, a lokacin rikicin hijabi da ya barke a makarantar Oyun Baptist High School, Ijagbo a karamar hukumar Oyun ta jihar.
Kungiyar ta kuma ce, ya kamata gwamnatin jihar Kwara ta nada sabon kwamishinan ma’aikatar ilimi a jihar.
Ta kuma bayyana cewa, ya zama wajibi gwamnatin jihar Kwara ta tabbatar da ‘yancin yin ibada a makarantu, kuma hana duk wani Limami ko Fasto daga wajen makaranta, ya shiga ibadar da ake gudanar wa da safiya, baya ga malaman makarantu.
A karshe kungiyar ta ce ya kamata gwamnati ta tabbatar da cewa nade-naden shugabannin makarantu a jihar kasance bisa cancanta da girma kuma ya zama alhakin hukumar kula da koyarwa ta jihar Kwara ce.