Mai Neman Takarar Gwamnan Jihar Katsina kuma Sakataren Gwamnatin Jihar Mai ci Dr.Mustapha Muh’d Inuwa, ya bukaci magoya bayanshi akan kada su damu da masu yi mashi sharri da kazafi akan harkokin Siyasar shi.
Dr. Mustapha Inuwa ya bayyana haka ne a lokacinda yake Jawabi ga daruruwan ya’yan Kungiyoyi da suke goyon bayan tsayawa takarar shi.
KARANTA WANNAN LABARIN: Kwamitin Tsare-tsare na Ganduje ya jaddada wa mambobin APC ƙarfin gwuiwar shirya Babban Taro — Cewar Buni
Kamar yadda ya bayyana, masu maganganun batanci a kanshi ba wani abu bane a zukatansu illa hassada da neman bata mashi suna a siyasance don su cimma kudurorinsu na son zuciya.
Alhaji Mustapha Inuwa ya tabbatar da cewa batun baya suna akan shi ba abu bane da aka fara a yanzu, kuma hakan bai hana shi cigaba ba ta fannonin rayuwa da siyasa.
“Don haka kada ku damu da duk wani da kika ji yana yarfen siyasa a kaina” Cewar Dr. Mustapha Inuwa.
Daga nan sai ya nuna godiyarsa ga Kungiyoyin akan yadda suka lura da nagartarshi ta neman Kujerar Gwamnan Jihar Katsina kuma suka nemi ya yi takara a 2023.
Sakataren Gwamnatin daga nan sai ya yi fatan idan shine alkairi ga Jihar Katsina Allah ya tabbatar da shi, idan kuma akasin hakan to Allah ya tabbatar da mafi Alkairi ga Jihar.
Comments 1