Musulmai sun koka kan hana su rajistar Katin Zaɓe a Adamawa
Ƙungiyar Al’ummar Musulmin Najeriya reshen Jahar Adamawa ta yi zargin hana Musulmi su riƙa yin rajistar Katin Zaɓe da ake gudanarwa a wasu Al’ummomi.
Da yake jawabi ga Manema labaru bayan taron gaggawa da Shuwagabannin daga Ƙananan Hukumomi 21 a Yola, a Jiya, Shugaban Malam Gambo Jika yace irin wannan al’amari yana faruwa ne musamman inda musulmi basu da yawa.
KARANTA WANNAN LABARIN: Shugaban Hukumar FRSC Marshal , Boboye Oyeyemi Yayi Murabus
A cewar sa, Majalisar ta gano inda ƴan Bigilanti da wasu ke cin zarafin Musulmai tare da hana su zaɓen Kananan Da rajistar Katin Zaɓe da ake gudanar wa.
“Mu Musulmin Jahar Adamawa mun kira wannan taron ne domin tattaunawa tare da gano yadda zamu magance wasu matsaloli a Jahar dama Najeriya baki ɗaya, musamman akan batun da ya shafi rajistar Katin Zaɓe da yanzu ya zama faɗa.
“Akwai wurare da dama a a jahar inda musulmi ba’a basu dama domin suje suyi zaɓe, bayan sun yi rajistar Katin Zaɓe. A wasu lokutan, ƴan Ƙungiyar Bigilanti marasa kishi ana amfani dasu domin cin zarafin mutane cewa kada su je Akwatunan Zaɓe na yankunan su.
“Muna kira ga Jami’an tsaro, da Shuwagabannin gargajiya, da Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta INEC dasu tabbatar cewa an baiwa mutane dama domin Kada kuri’ar su ko yin rajista ba tare da cin zarafi ba”, Cewar Jika.
Jika yayi kira ga Gwamnatin Jaha da Jami’an tsaro dasu tashi tsaye tare da kare hakkin ƴan ƙasa kafin wannan lamari ya haddasa faɗa
A lokacin da aka tuntuɓe shi, Mai Magana da Yawun Rundunar Ƴan Sandan Jahar SP Suleiman Nguroje yace basu san da wannan ba, yana mai shan alwashin gano lamarin tare da sanar dashi.