Musulman Kwara sun buƙaci a canja Sunan Makarantar da aka yi rikicin Hijabi
Al’ummar Musulmin Jahar Kwara sun buƙaci a canja sunayen Makarantun da Musulmai da Kiristoci ke Mallakin su a Jahar, a matsayin wani ƙoƙari na magance rikicin Sanya Hijabi a Jahar.
Musulman a cikin wata takarda da suka aike wa Gwamnan Jahar AbdulRahman AbdulRazaq, sun bada shawarwari guda 6 da suke so Gwamnati ta ɗauka domin magance rikicin sanya Hijabi ga Ɗalibai Mata a Dukkanin Makarantun Gwamnati a Jahar.
KARANTA WANNAN LABARIN: Ƴan Bindiga Sun Hallaka Ɗaliba zata zana Jarabawar WASSCE a Benue
“Gwamnatin Jahar Kwara akwai buƙatar ta canja sunayen Makarantun da Musulmai da Kiristoci suke Mallakin su misali ; makarantar Sakandare ta Ansarul Islam, Ilorin, da Bishop Smith Memorial Government College, Ilori,” Al’ummar Musulman sun bayyana a takardar.
Kwafin takardar mai kwanan watan 7 ga watan yuni na Shekarar 2022 da lamba ta KWS/MS/01/22 ɗauke dasa hannun Ishaq Abdulkareem (Shugaba) da Farfesa Ibrahim Abikan (Sakatare) da aka fitar wa Manema labaru a Ilori, Babban Birnin Jahar a ranar Litinin.
Musulman sun buƙaci a biya diyyar marigayi Habeeb Idris da aka kashe a ranar 3 ga watan Fabrairu na Shekarar 2022 a lokacin rikicin Hijabin daya faru a Makarantar Oyun Baptist Dake Ijagbo a Ƙaramar Hukumar Oyun ta Jahar.
Comments 1