Mutane 10 aka kashe a rana ta biyu na hare-haren jiragen sama a yankin Tigray na kasar Habasha a ranar Larabar nan, in ji wani jami’in asibiti, a hare-haren da suka biyo bayan hukumomin kasar sun bayyana shirin tsagaita wuta.
Hare-haren da jiragen yaki marasa matuka guda biyu suka kai a wata unguwa da ke Mekele babban birnin yankin, inda suka kashe mutane 10 tare da raunata wasu, in ji Kibrom Gebreselassie, babban jami’i a asibitin Ayder Referral, mafi girma a yankin Tigray.
Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa, Kibrom ya shaidawa kamfanin dilancin labaren AFP ta hanyar saƙon rubutu bayan da ya bayar da rahoton mutuwar mutane 6 tare da raunata fiye da 10 a tashin bama-bamai biyu da misalin karfe 7:30 na safe (04:30 GMT).
Dimokuradiyya ta rawaito cewa, Fasika Amdeslasie, wata likitar tiyata a wannan asibiti, ta ce harin bam na farko ya raunata wasu mata biyu, sannan kuma wani hari na biyu da jiragen dakon kaya suka yi kan mutanen da suka taru domin taimakawa wadanda abin ya shafa.
Karanta kuma: Yan Awaren Tigray Na Zargin Gwamnatin Habasha Da Kai Musu Hari
“A cikin wadanda abin ya shafa, wani uba ya mutu kuma an kai dansa tiyata,” in ji shi a shafin Twitter.
Tun da farko, mai magana da yawun kungiyar ‘yan tawayen Tigray People’s Liberation Front (TPLF) da ke yaki da gwamnatin Habasha kusan shekaru biyu, ya ce an kashe fararen hula da raunata wasu a harin amma bai bayar da karin bayani ba.
Kamfanin dillancin labaran AFP ya ce, ba ta iya tabbatar da ikirarin da kanta ba, yana mai karawa da cewa an takaita zirga-zirgar zuwa arewacin Habasha, kuma yankin Tigray ya kasance cikin katsewar hanyar sadarwa sama da shekara guda.
Harin da aka ruwaito ya biyo bayan wani harin da jiragen yaki mara matuki suka kai a ranar Talata a jami’ar Mekele, wanda kungiyar ta TPLF ta ce ya haddasa raunuka da kuma asarar dukiya.
Dimtsi Wayane, wani gidan Talabijin mai alaka da kungiyar TPLF da ke watsa shirye-shirye a yankin Tigrai, ya ce an kuma kai wa gidan rediyon hari a ranar Talata, lamarin da ya tilasta masa barin yada labarai.
Fira minista Abiy Ahmed gwamnatin kasar ba ta ce uffan ba game da tashin bama-bamai da aka bayar a wannan makon, kuma ba a amsa bukatar kamfanin dillancin labarai na AFP daga jami’ai ba.
A wani labarin kuma: Majalisar Dattawa Ta Fara Binciken Satar Mai A Yankin Niger-Delta
Kwamitin majalisar dattawa mai kula da satar mai na Adhoc, ya ce ya fara bincike kan al’amuran da suka shafi satar mai da ayyukan da ba bisa ka’ida ba a yankin Neja Delta.
Shugaban kwamitin, Bassey Akpan ne ya bayyana haka a lokacin da yake amsa tambayoyi daga ‘yan jarida a lokacin da suka isa filin jirgin sama na Fatakwal cikin mako.