A kalla mutane 10 ne suka kwanta dama bayan cin tuwon dawa mai dauke da guba a kauyen Jangeme dake karamar hukumar Gusau ta jihar Zamfara.
Mutane kusan dukkanin su yan gida daya ne kuma kananan yara dake tsakanin sherkara biyar zuwa sha biyu.
Yaran sun ɗirki tuwon dawar ne, bayan da aka yi kuskuren dafa shi da guba.
Wata yar yaran mai shekara 35 ce ta dafa tuwon da gubar bayan kai musu ziyara, wanda a tunaninta jar kanwa ce.
Da yake tabbatar da aukuwar wannan lamari ga manema labarai, Kakakin babban asibitin garin Yeriman Bakura , Auwal Ruwan Doruwa ya ce daya daga cikin yaran ya mutu ne a gida, gabannin garzayawa da sauran taran izuwa asibiti
A cewar sa uku kuma daga cikinsu sun mutu ne a daren ranar Litinin uku a Talata, biyu kuma ranar Alhamis yayin da sauram mutum guda ya rasu a ranar juma’a.