Akalla mutane 12 ne suka mutu sakamakon fashewar wasu tagwayen bama-bamai da aka kai da wata mota a hedikwatar karamar hukumar da ke Beledweyne, babban birnin lardin Hiran na Somaliya.
Hukumomin kasar sun ce wasu 10 sun jikkata, kana wasu gine-gine suka ruguje sakamakon fashe-fashen.
KARANTA WANNAN LABARIN: Shugaba Buhari Ya Nada Umar-Sadik A Matsayin MD Na Hukumar NSIA
Rundunar ‘yan sandan ta ce ministan lafiya na jihar da mataimakin hakimin gundumar na cikin wadanda suka mutu.
Kungiyar masu kaifin kishin Islama ta al-Shabab ta dauki alhakin lamarin. A baya-bayan nan ne ake gudanar da gangamin yaki da masu tada kayar baya da ke da alaka da al-Qa’ida.
An kashe shugaban al-Shabab
Ana kyautata zaton harin kunar bakin waken na iya kasancewa ramuwar gayya ne a karshen mako da aka yi wa wani babban jigo na kungiyar Al-Shabab a wani harin da aka kai da jiragen sama marasa matuka.
Hukumomin kasar sun sanar ‘yan sa’o’i kadan cewa an kashe Abdullahi Nadir, wanda aka yi masa ladar dala miliyan $3 , a wani farmakin hadin gwiwa da sojojin kasar Somaliya da na kawancen kasashen duniya suka kai.
Ba a dai bayyana ko su waye suka taimaka a wannan farmakin ba, amma sojojin kasar Somaliya na samun goyon bayan sojojin Amurka da kuma tawagar wanzar da zaman lafiya ta Tarayyar Afirka.
A baya-bayan nan ne Somaliya ta shelanta yaki da ‘yan ta’addar al-Shabab da ke rike da yankuna da dama a kudanci da kuma tsakiyar kasar.
A wani labarin kuma, Mutum Uku Sun Mutu A Hatsarin Mota A Kaduna
Wani hatsari da ya rutsa da motar Toyota Corolla a ranar Litinin ya halaka mutum uku daga cikin fasinjoji shida da ke cikin motar bayan motar ta kwace daga hannun matukinta
Daily Post ta ruwaito cewa, motar tana kan hanyar zuwa Kachia ne a lokacin da a rasa yadda za ta yi, kuma ta ci karo da wani rami.