Hukumar Inshorar Lafiya ta Kasa, NHIS ta fara daukar mutane 1,300 da za su ci gajiyar aikin kiwon lafiya kyauta na tsawon shekaru biyu a Zariya, Jihar Kaduna.
Sakataren zartarwa na NHIS, Farfesa Nasir Mohammed Sambo ya ce yayin kaddamar da shirin mai taken “Aikin Mazabar Zariya ta 2021 a Zariya,” a fadar mai martaba Sarkin Zariya, za a fitar da wadanda za su ci gajiyar shirin ne daga sassa masu rauni na al’umma da ba za su iya biya kudade ba, domin yin rajista a cikin tsarin.
Sambo ya ce gwamnatin tarayya ta yi tanadin kasafin kudi domin tabbatar da cewa an yi wa marasa galihu ta hanyar inshora aikin kiwon lafiya kyauta, inda ya ce za a tsawaita mazabar NHIS a duk sassan kasar nan.
Ya kuma yi kira da a hada kai da jihohi da kananan hukumomi da masu hannu da shuni domin kara fadada aikin fiye da yadda ake bukata.
Ya ci gaba da cewa, wani Asusun Tallafawa Kiwon Lafiya a matakin farko wato mai suna Basic Health Care Fund a turance, zai zo ta hannun gwamnatocin jihohi don kara kaimi wajen samar da hanyoyin kiwon lafiya ga marasa galihu. A cewarsa, “A shekarar da ta gabata, NHIS ta baiwa gwamnatin jihar Kaduna kudi naira miliyan 500 domin samar da lafiya ga marasa galihu a jihar.”
A nasa martanin, Sarkin Zazzau, Ambasada Ahmed Nuhu Bamalli, ya ce babu wani shiri da ya fi dacewa da zai kawo taimako ga marasa galihu kamar samar musu da kiwon lafiya kyauta.
Sarkin ya umurci shugabannin kananan hukumomin Masarautar da su shiga cikin shirin ta hanyar daukar nauyin karin mutane tare da tsawaita wa’adin akalla shekaru biyar na ayyukan kyauta.