• Yan bindiga 14 ne aka ake a harin da su ka yi kokarin kai wa ofishin rundunar yan sandan jihar Benue.
• Jami’in Hulda da jama’a na rundunar yan sandan jihar Benue ya tabbatar da afkuwar lamarin.
• “Al’umar garin Katsina-Ala su kwantar da hankulan su”, inji Kate.
Rundunar yan sandan jihar Benue ta tabbatar da kashe yan bindiga 14 a wani musayan wuta da jami’an ta su kayi da yan bindiga, lokacin da suka yi kokarin kai hari a ofishin yan sanda dake yankin Katsina-Ala a jihar, a safiyar yau lahadi.
Mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar DSP Kate Anne, ya tabbatar da afkuwar lamarin inda yace,”a ranar asabar, an kame wasu mutane da ake zargin yan bindiga ne, kuma aka kulle su a ofishin yan sandan dake Katsina-Ala, domin gudanar da bincike.”
Inda ya kara da cewa, a safiyar yau lahadi da musalin karfe 1, wasu yan bindiga da yawar su ya Kai 50, sun kai wani hari, a kokarin su, na kubutar da wadanda aka garkame.
Jami’in ya kuma ce, jami’an dake aiki a ofishin sun mai da wa yan bindigan martani inda su ka yi nasarar kashe 14 daga ci, wasu kuma suka tsere da raunikan harbin bindiga.
KARANTA WANNAN LABARIN: An sake nada Amina a matsayin mataimakiyar sakataran majalissar dinkin
A karshe, rundunar yan sandan jihar ta shawarci al’umar garin Katsina-Ala, dasu kwantar da hankulan su, kuma su cigaba da bai wa jami’an yan sandan bayanai.