Mutane 15 daga cikin wadanda aka kama a garin Tegina sun kubuto
Kimanin mutane sha biyar ne suka tsero daga hannun Yan bindaga cikin Mutanen da aka kwashe a garin Tegina dake jihar Neja.
Mutane Sha biyar suna daga cikin Mutanen da aka kwashe tare da Dalibai 156 na Makarantar Salihu Tanko Islamiyya dake garin Tegina.
KARANTA:- Wata budurwa ta boye kanta ta bukaci 500,000 kudin fansa
Jaridar Thisday ta hakaito Mutanen da aka kama tare da Daliban sun rabasu, inda manya aka tafi dasu dajin Zamfara su kuma Yaran ba’a san katamaiman inda aka aje su ba.
A daren Juma’a ne Mutanen suka samu damar kubu cewa saboda Yan bindigan da aka sanya tsaron su sunyi marisa.
Jaridar Thisday ta ruwaito lokacin da Mutanen suka tsere kowa yabi hanyar sa daban saboda kada Yan bindigan suji tafiyar su.
Mutumin daya fara isowa gari yake sanar da mahukunta nan take suka shiga cikin dajin don agazama sauran.
Shi kuma nan take aka kaishi asibiti don duba lafiyar shi.
Labari yazo cikin wadanda aka sace akwai kansila da direba a cewar wanda ya isa Tegina da safiyar Lahadi.