A karon farko an tabbatar da cewa a kalla mutane kimanin 154 ne suka sake harbuwa da cutar korona a Najeriya bayan cutar ta sake dawowa karo na uku a kasar.
Yanzu haka dai wannan adadi ya sanya halin ɗar-ɗar zukatar yan kasar da ta kasance ta farko da ta fara saun cutar a kasashen Afirka ta yamma a watan Fabrairun bara.
A ranar talata ne dai hukumar dake kula da cututtuka masu yaɗuwa ta NCDC ta sanar da hakan cikin kididdigar masu dauke da cutar da ta saba fitarwa kowace rana.
Jihar Legas wacce ita ce jiha da cutar ta fi yiwa illa a karon farko da na biyu, har yanzu ita ce ke jan zarenta a wannan karo.
A yanzu haka dai jihar ita kaɗai tana da adadin mutane 119 cikin adadin da NCDC ta fitar, yayin da jihar Akwa Ibom ke biye mata da mutane 11.
Har wa yau akwai wasu jihohi shida kamar su Rivers dake da shida sai Oyo mai biyar yayin da Ekiti da Ogun da birnin tarayya Abuja kowannen su ke da huɗu sai Gombe mai biyi da kuma Kwara dake da guda.