By Abbas Yakubu Yaura
Mutane 17 ne suka mutu yayin da 14 daga cikinsu suka kone kurmus bayan da wata tankar mai ta fashe da safiyar Juma’a a babbar hanyar Legas zuwa Ibadan.
Hadarin ya afku ne da misalin karfe 5:00 na safe a bakin gadar Isara ta babban titin tare da wasu motoci guda biyu masu lamba ZT728 KLD(Mazda Bus) da wata tankar da bata bayyana ba.
An ce motocin sun yi taho-mu-gama ne sakamakon tukin ganganci, lamarin da ya haifar da fashewar wani abu da ya rutsa da fasinjojin da ke cikin motar bas ta Mazda.
Da take tabbatar da aukuwar lamarin, hukumar kiyaye hadurra ta kasa (FRSC), reshen jihar Ogun, ta ce an sanar da sashen ‘yan sanda na Isara da dakin ajiye gawa na FOS gabanin shirin kwashe wadanda suka mutu.
Sufeto na (SRC) Florence Okpe, wacce ita ce jami’ar FRSC mai kula da sashen ilimin jama’a na rundunar hukumar ta jihar Ogun, Umar Ahmed, ta alakanta musabbabin hatsarin da keta haddin hanya da tukin mota mai hatsari, wanda ya yi sanadin yin karo da tada gobara.
“Ba a tantance adadin mutanen da lamarin ya shafa ba amma an gano gawarwaki 17 (da suka mutu ).sannan an gano wani yaro namiji daya mace daya yayin da wasu kuma suka kone ba a iya gane su kuma babu wani rauni da suka samu.
“Musabbabin abinda ake zargin ya haddasa hadarin sun hada da keta haddin hanya da tukin mota wanda ya yi sanadin yin karo da tada gobara.
“Motocin suna dakile wani bangare na hanyar sabis. An sanar da ‘yan sandan Isara da FOS Morgue ta ma’aikata Isara. Jami’an hukumar FRSC daga Ogere suna nan a kasa suna gudanar da lamarin aikin ceto.
“Kwamandan sashin FRSC Ogun ya bayyana hatsarin a matsayin abin da za a iya kaucewa idan aka yi taka-tsantsan da kuma bin ka’idojin zirga-zirga.sannan ya jajantawa iyalan wadanda hatsarin ya rutsa da su, ya kuma umurce su da su tuntubi FRSC Ogere don karin bayani game da hadarin,” inji ta.