Akalla matasa 17 ne aka tsinci gawarwakinsu a wani gidan rawa dake garin Birnin London na kudancin Afirka ta Kudu ranar Lahadi, in ji ‘yan sandan kasar
“Mun samu rahoto game da mutane 17 da suka mutu a wani wurin shakatawa na Scenery Park wanda ke gabashin London,” in ji wani babban jami’in ‘yan sanda na lardin, kammar yadda Birgediya Thembinkosi Kinana ya shaida wa kamfanin Dillancin Labaran faransaAFP.
Ya ce wadanda abin ya shafa na da shekaru tsakanin 18 zuwa 20.
Hotunan da ba a tantance ba da aka yada a shafukan sada zumunta sun nuna gawarwakin da ba a ga alamun raunuka ajikin su ba,, sun baje a kasa a filin kulob din.
Gidan talabijin na kasar ya nuna jami’an ‘yan sanda kasar na kokarin kwantar da hankulan gungun mutanen da suka taru a wajen kulab din da ke birnin, wanda ke gabar tekun Indiya, mai tazarar kusan kilomita 1,000 (mil 620) da kudancin Johannesburg.