Hukumar tsaro ta NSCDC reshen jihar Kaduna ta ce ta kama mutum 19 bisa zargin aikata Fyaɗe a jihar tsakanin watan Agusta da Satumba.
Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da majalisar dokokin jihar ta yi dokar dandaƙe masu fyaɗe wadda gwamna Nasir El-Rufai ya rattaba wa hannu.
Kakakin rundunar, ASC Orndiir Terzungwe shi ne ya bayyana hakan yayin da yake ganawa da manema labarai a hedikwatar rundunar da ke Kaduna ranar Juma’a.
Ya ce ana zargin mafi yawan waɗanda aka kama ne da lalata yara ƙanana.
Orndiir ya ce, “A ƙoƙarinmu na rage yi wa yara ƙanana fyaɗe, NSCDC a jihar Kaduna ta samu nasarar cafke aƙalla mutum 19 daga watan Agusta zuwa yau.
“Idan an lura sosai za a fahimci cewa rundunarmu na neman tallafin jama’a a ko da yaushe, kuma muna godiya da yadda suke ba mu tallafi.
“Sai dai abin takaicin shi ne kusan dukkannin waɗanda lamarin ya shafa ƙananan yara ne”, inji shi.
Ya ce wasu daga cikin yaran sun kamu da cututtuka, kuma an gurfanar da 18 daga cikinsu waɗanda ake zargin a gaban kuliya tare da ƙwarin gwiwar cewa kotun za ta aike da su gidan kaso.
“Abin takaici ne matuƙa yadda ake samun wannan matsalar duk da irin tsauraran dokokin da gwamnatin jihar Kaduna ke yi kan masu aikata laifin.
“Za mu ci gaba da yin duk abin da yake a bisa doron doka wajen ganin mun magance hakan,” inji shi.