An tabbatar da mutuwar mutane 19 yayin da wasu 8 suka jikkata a wani mummunan hatsarin mota da ya afku a ranar Lahadi a hanyar Yangoji zuwa Gwagwalada a babban birnin tarayya Abuja.
Mista Dauda Biu, mai rikon mukamin Marshal na hukumar kiyaye hadurra ta kasa (FRSC), ya tabbatarwa kamfanin dillancin labarai na kasa NAN alkaluman lokacin da ya ziyarci wurin da hatsarin ya afku.
KARANTA WANNAN LABARIN: Zan Jagoranci Najeriya Na Ciyar Da Ita Gaba Da Hikima – Atiku
Biu ya ce hatsarin wanda ya faru mintuna kadan cikin ranar Lahadi ya hada da motoci uku – motocin bas Toyota Hiace guda biyu masu lambar rajista MUB- 30 LG da DWR-985 XJ da wata mota kirar fasaha.
Biu ya ce mutane 31 ne hatsarin ya rutsa da su da suka hada da maza 11, mace daya da kuma wasu 19 wadanda suka kama da wuta.
“A cikin mutane 31 da abin ya shafa, mutum takwas da suka hada da maza bakwai da mace daya sun samu raunuka daban-daban, yayin da wasu 19 suka kone kurmus.”
“Bincike ya nuna cewa manyan abubuwan da suka haddasa hadarin sun hada da gudun wuce sa’a da kuma wuce gona da iri wanda a karshe ya haifar da asarar Rayuka,” in ji shi.
A cewarsa, motar kirar Toyota Hiace mai lamba MUB- 30 LG, ta afka cikin motar kirar Citroen tare da barkewar wuta, inda duk wanda ke cikin motar sun mutu.
“Bas na biyu ya bugi bas ta farko daga baya sannan kuma ta kama wuta. Gobarar ta narkar da motar bas ta biyu mai lambar jihar Bauchi.”
“Motar ta taho ne daga Takai, Jihar Kano yayin da yake kan hanyar zuwa Benin. Motar Citroen ta yi lodin kaji daga Zaria a jihar Kaduna inda ta nufi Akwa Ibom.
“Gawawwakin mutane goma sha tara sun makale amma jami’an ceto sun fitar da su,” inji Biu.
Ya kara da cewa ‘yan sanda sun dauki nauyin gudanar da binciken tare da ganawa da hukumomin da abin ya shafa domin binne gawarwakin mutane 18 da aka yanke.
Ya ce ba a iya adana gawarwakin domin tantancewa ba saboda sun kone ba a iya gane su.
“Ana ci gaba da share duk wani cikas na hana zirga-zirgar ababen hawa kamar yadda kuke gani kuma za mu yi iya kokarinmu don ganin mun samu al’umma da ba ta da hadari,” inji Biu ya shaida wa NAN.
“An kai wadanda suka jikkata zuwa wani asibiti da ke kusa da Kwali a babban birnin tarayya Abuja kuma an ajiye gawar namiji guda daya a dakin ajiye gawa a babban asibitin Kwali,” inji shi.
Biu ya gargadi masu amfani da hanyar da su guji, wuce gona da iri da sauran munanan halayen tuki. (NAN)
A wani labarin kuma, Da Dumi-dumi: Daya Daga Cikin Sarakuna Masu Zabar Alapinni Na Oyo Ya Rasu
Wani fitaccen dan majalissar sarki a Najeriya, Alapinni na Oyoland, Babban Hakimi, Alh Abdul-Rasheed Shehu ya rasu.
Rahotanni sun bayyana cewa, Alapinni na Oyo, wanda yana daya daga cikin Oyomesi (sarakunan da ke da alhakin zaben Alaafin na Oyo na gaba) ya rasu da sanyin safiyar Lahadi, 18 ga watan Satumba, 2022, bayan ya yi fama da rashin lafiya da ba a bayyana ba.